Shafin Hadisai

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinƙai. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga fiyayyen talikai Annabi Muhammadu da iyanlsa da sahabbansa.

Dukkan yabo da godiya na ga Allah Ubangijin dukkan halittu. Bayan haka assalamu alaikum warahmatullah.

Mai karatu, barka da shigowa wannan shafi mai tarin albarka. Shafi ne da ke ɗauke da kalaman (Hadisai) Manzon Allah (SAW), Annabi rahama, annabi da ba bu wani annabi bayansa. Annabin da Allah ya yiwa sheda da cewa ba ya furuci bisa son ransa sai abin da aka saukar masa (daga Allah).

Ina roƙa mana Allah ya bamu kunnuwa da basirar sauraron waɗannan maganganu na Manzon Allah (SAW) ya kuma bamu ikon yin aiki da abin da muka karanta. Haƙiƙa ya rabauta duk wanda ya zama rayuwarsa ta ɗoru bisa maganganun Manzan Allah (SAW).

ƙofa a buɗe take dan karɓar gyara da shawarwari. Latsa nan da saduwa da mu