Shafin Alƙur'ani Mai Tsarki

Matani:      Buɗe
Tarjama:    Sheikh A. M. Gumi
                    Sheikh M. N. Kabara
Tajwid:       Buɗe

Da sunan Allah Mairahama Maijinƙai. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga fiyayyen talikai Annabi Muhammadu da iyanlsa da sahabbansa.

Dukkan yabo da godiya na ga Allah Ubangijin dukkan halittu. Bayan haka assalamu alaikum warahmatullah.

Wannan Shafi da ka ke ciki yana ɗauke da abubuwan da suka shafi Alƙur'ani zancen Allah Mai Girma da Buwaya. Manufar shafin ita ce samar da hanya mai sauƙi da jama'ar Musulumi za su riƙa samun ilimin Alƙur'ani cikin sauƙi ta hanyar amfani da sabuwar hanyar sadarwa ta zamani. Alƙur'ani shi ne littafin da sauraron karanta shi ma lada ake samu.

Muna roƙon Allah ya sa wannan aiki ya zama mai amfani ga Musulunci da Musulmi baƙi, Ya ƙarawa Annabi daraja da kusanci, Ya gafarta mana dukkan zunubanmu, Ya yafe mana dukkan kurakuranmu, Ya albarkaci zuriyarmu, Ya ɗaukaka addinin Musulunci da Musulmi. Amin.