Shafin Littattafai

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinƙai. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga fiyayyen talikai Annabi Muhammadu da iyanlsa da sahabbansa.

Dukkan yabo da godiya na ga Allah Ubangijin dukkan halittu. Bayan haka assalamu alaikum warahmatullah.

Barka da buɗe katafaren ɗakin karatun littattafan Musulunci cikin harshen Hausa Zalla.

Wannan shafi ya ƙunshi littattafan Musulunci wanda za ka iya karantawa cikin Harshe Hausa. Shafi ne da za a riƙa sabunta shi ta hanyar ƙara masa littattafai a kodawane lokaci da zarara an samu cigaba. Saboda haka matuƙar kana son cin cikakkiyar moriyar wannan shafi, to sai ka mayar da shi abokin hirarka.

Allah, muna roƙon Ka, Ka karɓa mana wannan aiki. Ka albarkaci duk wanda ya karanta waɗannan littattafai da aiki da abubuwan da aka koya don kar ya zama hujja a kanmu kamar yadda na baya suka yi waɗanda suka zama kamar jaki da kaya a ka cikin faɗinSa Maɗaukakin Sarki:

مَثَلُ الَّذِينَ حُمِّلُوا التَّوْرَاةَ ثُمَّ لَمْ يَحْمِلُوهَا كَمَثَلِ الْحِمَارِ يَحْمِلُ أَسْفَارًا بِئْسَ مَثَلُ الْقَوْمِ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِ اللَّهِ وَاللَّهُ لا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ

Misalin waɗanda aka ɗora wa ɗaukar Attaura sa'an nan basu ɗauke ta ba, kamar misalin jakin ne, yana ɗaukar littattafai. Tir da misalin mutanen1 nan da suka ƙaryata game da ayoyin Allah! Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai. Fassarar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi (Suratul Jumu'at: 5).


1. Tir wanda ya yi siffa da irin siffofin Yahudu daga Musulmi wajen ɗaukar karatun Alƙur'ani amma kuma bai yi aiki da shi ba. Yahaya bn Yamani ya ce, "Suna rubuta hadisi basu fahimtarsa, kuma bas u kula da ma'anarsa". Watau suna wahala wajen ɗaukar ilmin da aka ɗora musu ɗaukarsa amma kuma ba su yin amfani da shi wajen aikinsu da mu'amalolinsu.