Shafin Farko

Maidarasu softuwayar Musulunci ce cikin harshen Hausa zalla wacce aka samar da ita tun cikin shekarar 2014 kuma aka ƙaddamar da ita a babban ɗakin taro na Gidan Mambayya bisa jagoranci Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Abdullahi Bayero da kuma Shugabancin gwamnatin jahar Kano ta Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso da wakilcin sarakunan Dutse da Zazzau da kuma na Jahar Kaduna da sauran manyan malamai kamar irin su Shehu Nasidi Abubakar Gwauron Dutse sannan kuma Farfesa Abdallah Uba Adamu ya gabatar da jawabi a wajen taron. Dukkaninsu da ma waɗanda ba mu ambata sunayensu ba daga cikin waɗanda suka bayar da gudunmawa muna rokon Allah ya riɓanya ladansu, ya kuma maye gurbin abubuwan da suka fitar ninkin ba ninki.

Muna kuma yi wa masu karatu albishir da sake bayyanar waɗannan shafuka a wannan duniya ta gaibu mai bayar da tarin gudunmawa wajen yaɗa ilimi da kuma sauƙaƙa bincike.

Duba izuwa ga yadda kwamfuta da sotwaya a yau suka zama sanadi na samun kowane irin ilimi cikin sauƙi, za mu ga cewa haƙiƙa irin waɗannan softwayar sun ƙaranta a Harshen Hausa ko kuma ma babu su sam-sam. Sai muka ga cewa zai yi matuƙar kyau mu yi amfani da wannan dama da muke da ita a yau mu samar da wannan softwaya da za ta taimaka wa Musulmi mai magana da Harshen Hausa wajen samun ilimin addinin Musulunci cikin Harshen Hausa.

Abubuwan da wannan softwaya ta ƙunsa a yanzu kamar na somin taɓi ne, amma muna da guri na ganin cewa zuwa nan gaba ta zama cikakkiyar ɗakin binciken ilimin addinin Musulunci da ma sauran ilimummukan da za su tai maka wajen yin haka. Wannan kuma muna da manufa ta, ta zama mai amfani ga kowa kamawa tun daga yara 'yan makaranta har zuwa kan ɗaliban ilimi kai har ma da malaman da ke buƙata a nan-da-can.

Muna fata wannan softwaya da kuma wannan shafi da ka ke ziyarta za su zama masu amfani gare mu baki ɗaya.

Ƙofar mu a buɗe take wajen karɓar gyara da shawarwari.